Gidan talabijin na gwamnatin Iran, IRIB, ya ruwaito cewa Iran ta kai hari kan wani sansanin sojin Amurka da ke ƙasar Kuwait.

A cewar kafar yaɗa labaran, an kai harin ne a tsibirin Bubiyan, wanda shi ne mafi girma a ƙasar Kuwait.

Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta bayyana harin a matsayin "martani mai ƙarfi" ga hare-haren da take zargin Amurka da kai wa Iran.

Rahoton ya kuma ce an ji wasu manyan fashe-fashe a wasu wurare da Iran ta bayyana a matsayin hedkwatar ƙungiyoyin adawa da gwamnatin ƙasar, waɗanda ta zargi da ayyukan ta'addanci.

A watannin baya-bayan nan, Iran ta sha kai hare-hare kan sansanonin ƙungiyoyin Kurdawan adawa da ke yankin Kurdistan na ƙasar Iraki, tana zargin su da barazana ga tsaron ƙasar.

Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan labari, ba a samu wata sanarwa daga gwamnatin Kuwait ko rundunar sojin Amurka da ta tabbatar da iƙirarin kai hari kan sansanin sojin Amurka da ke Kuwait ba. Don haka, har yanzu ba a tabbatar da wannan rahoto daga wata majiya mai zaman kanta ba.