Majalisar Dokokin Faransa ta amince da wani ƙudiri da zai ba da damar taimaka wa wasu marasa lafiya da ke cikin mawuyacin hali su kawo ƙarshen rayuwarsu, amma ƙarƙashin tsauraran sharuɗɗan doka.
Batun ya shafe shekaru yana jawo muhawara a ƙasar, inda a baya Majalisar Dattawa ta yi watsi da irin wannan ƙudiri sau da dama.
Idan ƙudirin ya zama doka, zai shafi manyan mutane da ke fama da cututtuka masu tsanani kuma marasa magani, waɗanda suka kai matakin ƙarshe ko kuma suke fuskantar matsananciyar azaba da magunguna ba sa iya rage musu raɗaɗi.
Ƙudirin ya tanadi cewa mara lafiyar ne zai sha maganin da zai kawo ƙarshen rayuwarsa da kansa. Sai dai idan yanayinsa bai ba shi damar yin hakan ba, likita ko mai kula da lafiyarsa na iya taimaka masa wajen aiwatar da hakan, bisa tanadin dokar.
Kafin ƙudirin ya zama cikakkiyar doka, za a miƙa wasu sassa nasa ga Majalisar Kare Kundin Tsarin Mulkin Faransa, domin tantance ko sun dace da kundin tsarin mulkin ƙasar.
Batun na ci gaba da haifar da muhawara tsakanin masu goyon bayan 'yancin mara lafiya ya yanke hukunci kan rayuwarsa, da kuma waɗanda ke adawa da shi bisa dalilai na ɗabi'a, addini da kuma aikin likitanci.