An ji ƙarar fashewar abubuwa a sassa daban-daban na Iran, ciki har da yankunan da ke kusa da Tekun Fasha, bayan da rundunar sojin Amurka ta sanar da ƙaddamar da wani sabon zagayen hare-hare.

A babban birnin ƙasar, Tehran, rahotanni sun ce an kunna na'urorin kariya daga hare-haren makamai masu linzami domin daƙile barazanar da ake fuskanta. Haka kuma, an ba da rahoton tashin hankali a birnin Ahvaz, da ke kudancin ƙasar kusa da Tekun Fasha.

Kafafen yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa an kwashe marasa lafiya daga wani asibiti da ke kusa da wuraren da aka kai hare-haren, domin kare lafiyarsu.

A wata sanarwa, babban mai shiga tsakani na Iran a tattaunawa da Amurka, Mohammed Bagher Qalibaf, ya ce ƙasarsa za ta ci gaba da haɗa tattaunawa da matakan soja, yana mai jaddada cewa Iran ba za ta yi watsi da ikon da take da'awar tana da shi kan mashigar ruwan Hormuz ba.

A nata ɓangaren, Iran ta ce mayar da martaninta ya fi karkata ne kan cibiyoyin sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya.

Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan labari, ba a samu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da cikakkun bayanan hare-haren da ɓangarorin biyu suka yi iƙirari a kai ba.