Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta sanar da ƙulla wata gagarumar yarjejeniya tsakanin Tarayyar Turai (EU) da Ukraine domin haɗa kai wajen ƙera jiragen sama marasa matuƙa (drones) na zamani.
A cewarta, yarjejeniyar ta haɗa da tallafin Euro biliyan guda, wanda za a yi amfani da shi wajen bunƙasa masana'antar ƙera jiragen marasa matuƙa da kuma ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ɓangarorin biyu.
Von der Leyen ta bayyana cewa shirin zai haɗa ƙwarewar da Ukraine ta samu a fagen fama tun bayan fara yaƙin da Rasha, da kuma ƙarfin masana'antun Tarayyar Turai wajen samar da ingantattun kayayyakin tsaro da fasahar zamani.
Ta ƙara da cewa haɗin gwiwar na da nufin ƙarfafa tsaron Turai baki ɗaya, tare da tallafa wa Ukraine wajen ci gaba da kare kanta a yayin da yaƙin da Rasha ke ci gaba.
Wannan yarjejeniya na daga cikin matakan da Tarayyar Turai ke ɗauka na ƙara zurfafa haɗin gwiwar tsaro da Ukraine, tare da bunƙasa samar da makamai da fasahohin kariya a nahiyar Turai.