Gwamnatin Jamhuriyar Chadi ta sanar da cewa za ta daina buƙatar takardar izinin shiga ƙasar (Visa) ga dukkan 'yan ƙasashen nahiyar Afirka, a wani mataki da ke da nufin ƙarfafa haɗin kan nahiyar da bunƙasa harkokin kasuwanci da zirga-zirgar jama'a.
A cewar gwamnatin Chadi, sabon tsarin zai fara aiki ne daga 1 ga watan Janairun shekarar 2027.
Mahukuntan ƙasar sun bayyana cewa matakin zai sauƙaƙa zirga-zirga tsakanin ƙasashen Afirka, ya ƙarfafa cinikayya, zuba jari, yawon buɗe ido da kuma mu'amalar diflomasiyya tsakanin al'ummomin nahiyar.
Ana kuma sa ran wannan tsari zai taimaka wajen aiwatar da manufofin haɗin kan Afirka da yarjejeniyar yankin ciniki cikin 'yanci ta Afirka (AfCFTA), wadda ke da burin ƙara haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin ƙasashen nahiyar.
Masana harkokin diflomasiyya na ganin cewa matakin na Chadi zai iya zama wani muhimmin ci gaba wajen sauƙaƙa zirga-zirgar 'yan Afirka da ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙasashen nahiyar.