Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya umarci Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya sauka daga muƙaminsa na wucin gadi har sai an kammala bincike kan mutuwar Mary Habila, wata matashiya mai shekara 26 da ta rasu a gidan ministan da ke Uburu, Jihar Ebonyi.
Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya nuna damuwa kan yadda ake gudanar da binciken lamarin.
Ya ce akwai buƙatar a tabbatar da cewa binciken ya kasance mai zaman kansa, gaskiya da kuma adalci, yana mai zargin cewa gwamnati ba ta nuna isasshen jajircewa wajen gano haƙiƙanin abin da ya faru ba.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi kira ga Sufeto Janar na ’Yan Sanda da ya mayar da binciken zuwa Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda ta Ƙasa, tare da haɗa ƙwararrun masana binciken kimiyya domin gudanar da bincike mai zurfi.
Baya ga haka, Atiku ya buƙaci a gudanar da cikakken gwajin gawa mai zaman kansa, a ba iyalan Mary Habila kariya daga duk wani nau’in matsin lamba, tare da tabbatar da cewa babu wani mai riƙe da muƙamin gwamnati da ya fi ƙarfin doka.
Ya ce ɗaukar waɗannan matakai zai ƙara tabbatar wa da jama’a cewa ana gudanar da binciken cikin gaskiya da adalci ba tare da katsalandan ba.