Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya buƙaci Adeniyi Adeyemi, wanda ake zargi da ikirarin jagorantar wata hukumar bogi a Nijeriya, ya biya shi diyyar Naira biliyan 15 kan zargin ɓata masa suna.


A cikin takardun ƙarar da aka shigar, Gbajabiamila ya ce kalamai da zarge-zargen da Adeyemi ya yi a kansa sun bata masa suna da mutunci, tare da jawo masa illa a idon jama’a.


Saboda haka, ya buƙaci kotu ta umarci Adeyemi da ya biya shi diyyar Naira biliyan 15 saboda abin da ya bayyana a matsayin ɓata suna, tare da bayar da wasu umarni da suka dace domin kare martabarsa.


Lamarin na zuwa ne yayin da Adeyemi ke fuskantar shari’a kan zargin ikirarin jagorantar wata hukuma da gwamnatin tarayya ba ta amince da ita ba.

Ana sa ran kotu za ta fara sauraron ƙarar bisa tsarin shari’a domin yanke hukunci kan buƙatun da aka gabatar.