Gwamnan Jihar Kano ya bai wa mahautan jihar tallafin Naira miliyan 100 tare da yin alkawarin gina musu sabuwar kasuwar zamani domin inganta harkokin kasuwancinsu.


Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin rabon tallafin kayan aiki ga mahauta 1,900 daga sassa daban-daban na jihar. Ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen ƙarfafa sana’o’in da ke samar da ayyukan yi da kuma ƙara wa al’umma hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.


A cewarsa, tallafin da ake bai wa mahautan da kuma shirin gina kasuwar zamani na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka na bunƙasa ƙananan sana’o’i da inganta tattalin arzikin Kano.


Ya ƙara da cewa gwamnatin da za ta ci gaba da ƙaddamar da shirye-shiryen tallafa wa masu sana’o’i domin inganta rayuwarsu da haɓaka kasuwanci a faɗin jihar.