Ofishin jakadancin Faransa a Kamaru ya fitar da sanarwa da ke bayyana cewar, ya ɗauki matakin tsaurara ƙa’idojin bai wa ɗaliban biza ne saboda ta’azzarar almundahana a tsarin.
Wannan ya biyo bayan zanga-zangar da ɗimbin mutane su ka yi a gaban ofishin jakadancin Faransa da ke Yaounde, don nuna adawar su da sabon matakin.
Muriel Piquet-Viaux, guda cikin jami’an diflomasiyyar Faransa, ta ce ɗaukar matakin ya zama dole, saboda yadda ake cusa takardun ɗalibai na bogi domin gamsar da ƙasar wajen basu izinin yin karatu a Paris.
A cewarta, yanzu sun samar da sabon tsarin da ya ƙunshi buƙatar ɗalibi ya bayyana shaidar biyan kuɗin makarantar da zai yi karatu a Faransa, ko kuma basu shaidar cewar ya mallaki wannan adadin kuɗin kafin a bashi biza.
Kamaru, ita kaɗai ce ƙasa daga Nahiyar Afrika da hukumomin Faransa suka ɗauki irin wannan mataki dangane da karatun ɗaliban Yaounde a ƙasar ta Turai, lamarin da bai yi wa iyalai da da dama daɗi ba.