Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙaddamar da wasu manyan shirye-shirye biyar da darajarsu ta kai kusan dala biliyan 3.05, domin rage talauci, ƙarfafa al’umma da bunƙasa jarin ɗan Adam a Nijeriya.
An ƙaddamar da shirye-shiryen ne a ranar Alhamis a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda Ministan Kuɗi da Harkokin Tattalin Arziƙi, Wale Edun, ya wakilci shugaban ƙasa.
Shirye-shiryen sun haɗa da NG-CARES Additional Financing, wanda aka tsara domin tallafa wa tattalin arziƙin al’umma da waɗanda suka rasa matsugunansu, da kuma shirye-shiryen HOPE-GOV, HOPE-PHC, HOPE-EDU da SOLID, waɗanda za su mayar da hankali kan inganta shugabanci, kiwon lafiya da ilimi.
A cikin saƙonsa, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa waɗannan shirye-shirye ba wasu ayyuka ne daban-daban ba, illa wani tsari guda na ƙasa da aka ƙirƙira domin rage talauci, bunƙasa jarin ɗan Adam da ƙarfafa juriyar al’umma.
Ya ce shirin NG-CARES zai samu ƙarin tallafin dala biliyan 1.25 daga Bankin Duniya domin tallafa wa ƙananan manoma da ƙananan ’yan kasuwa.
Haka kuma, shirin SOLID zai samu dala miliyan 300 domin taimaka wa ‘yan gudun hijira da kuma al’ummomin da ke karɓar waɗanda suka rasa matsugunansu.
Shugaban ya ƙara da cewa kunshin shirye-shiryen HOPE, wanda darajarsa ta kai dala biliyan 1.5, zai taimaka wajen inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, bunƙasa ilimin firamare da kuma tallafa wa malamai.
Da yake jawabi, Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi, Atiku Bagudu, ya bayyana shirye-shiryen a matsayin wani cikakken martani na gwamnati ga matsalolin talauci, tsadar rayuwa da ƙalubalen bunƙasa jarin ɗan Adam.
Shi ma Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya ce shirin HOPE-PHC, mai darajar dala miliyan 570, zai inganta ayyukan kiwon lafiya na matakin farko ga kusan ’yan Nijeriya miliyan 40, musamman mata, yara da matasa.
A nasa ɓangaren, Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya bayyana cewa shirin HOPE-EDU, wanda ya kai dala miliyan 562, zai amfanar da kusan ɗalibai miliyan 30, tare da tallafa wa malamai 500,000 da kuma ƙarfafa makarantu gwamnati 65,000 a faɗin ƙasar.
Shugaban Bankin Duniya a Nijeriya, Matthew Verghis, ya ce shirye-shiryen sun nuna cewa mafi girman arzikin Nijeriya shi ne al’ummarta, yana mai tabbatar da cewa bankin zai ci gaba da tallafa wa sauye-sauyen da za su inganta ilimi, kiwon lafiya da tsarin tallafin jama’a.
Gwamnatin Tarayya ta kuma bayyana cewa ƙarin shirin tallafin kuɗi kai tsaye ya riga ya isa ga gidaje marasa galihu miliyan 15, tare da kira ga gwamnatocin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi, da kuma abokan hulɗar ci gaba su haɗa kai wajen tabbatar da aiwatar da shirye-shiryen yadda ya kamata.