Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin ƙwace wasu kadarori da kuɗaɗe da suka haura dala miliyan biyu da ake dangantawa da tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Hukuncin ya tabbatar da matakin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke a baya na ƙwace kadarorin, bayan da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gabatar da hujjojin da ke nuna cewa ana zargin an mallaki kadarorin ne ta hanyar da ta saɓa wa doka.
Kotun Koli ta amince da hukuncin da kotun ƙasa ta yanke, wanda hakan ya tabbatar da cewa kadarorin da kuɗaɗen za su kasance mallakin gwamnatin tarayya bisa tanadin doka.
Shari’ar na daga cikin matakan da EFCC ke ɗauka na bin diddigin kadarorin da ake zargin an samu ta hanyar da ba ta dace ba, yayin da ake ci gaba da gurfanar da Emefiele kan wasu zarge-zargen cin hanci da rashawa da almundahanar kuɗi, zarge-zargen da ya musanta.