Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da wasu shugabannin Jam'iyyar PDP suka shigar, wadda ke neman a tilasta wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta amince da kwamitin riƙon ƙwaryar jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki.

Mai Shari'a Salim Ibrahim ya yanke hukuncin cewa masu shigar da ƙarar ba su da hurumin gabatar da ita, saboda haka kotun ba ta da ikon sauraron shari'ar.

Alƙalin ya bayyana cewa masu ƙarar sun kasa gabatar da hujjojin da ke nuna cewa INEC ta taɓa amincewa da kwamitin riƙon ƙwaryar da suke goyon baya, ko kuma cewa suna da ikon shigar da ƙara a madadin jam'iyyar PDP.

Shugaban Kwamitin Amintattu na PDP na ɓangaren Kabiru Turaki, ƙarƙashin jagorancin Sanata Adolphus Wabara, tare da wasu mambobin kwamitin, ne suka shigar da ƙarar. Sun buƙaci kotun ta umarci INEC ta sabunta bayananta tare da amincewa da kwamitin riƙon ƙwaryar, sannan ta wallafa sunayen shugabanninsa a shafin yanar gizon hukumar.

Sai dai wani ɓangaren jam'iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Abdulrahman Mohammed, wanda ke samun goyon bayan Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya nemi shiga cikin shari'ar tare da ƙalubalantar hurumin kotun.

Wannan ɓangaren ya yi iƙirarin cewa shi ne halastaccen shugabancin jam'iyyar PDP, kuma masu shigar da ƙarar ba su da ikon wakiltar jam'iyyar a gaban kotu.