Gwamnatin Amurka ƙarƙashin Shugaba Donald Trump ta sanar da sabbin ƙa'idoji da za su tsaurara dokokin zama da karatu ga ɗaliban ƙasashen waje da ke ƙasar.
Sabbin dokokin, waɗanda za su fara aiki daga watan Satumba, sun haɗa da ƙayyade tsawon lokacin zama, da kuma takaita damar ɗalibai na sauya fannin karatu ko canza jami'a.
A baya, jami'o'in Amurka ne ke da ikon tsawaita wa ɗalibai wa'adin zamansu bisa tsarin bizar karatu. Sai dai a ƙarƙashin sabon tsari, wannan iko zai koma hannun Gwamnatin Tarayya.
Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka ta bayyana cewa sabbin matakan na da nufin hana amfani da bizar ɗalibai ba bisa ƙa'ida ba, tare da ƙarfafa tsaron ƙasa ta hanyar ƙara sa ido kan masu irin waɗannan biza.
Muhimman sauye-sauyen da sabbin ƙa'idojin suka ƙunsa:
- Ba za a ba ɗaliban ƙasashen waje damar zama a Amurka fiye da shekara huɗu ba, sai idan gwamnatin tarayya ta ba da ƙarin izini.
- Za a takaita damar sauya fannin karatu ko kuma canza jami'a ko kwaleji.
- Gwamnatin tarayya ce kaɗai za ta riƙe ikon tsawaita wa'adin bizar ɗalibai, maimakon jami'o'i.
- Bayan kammala karatu, ɗalibi zai samu kwana 30 kacal ya bar Amurka ko ya sauya nau'in bizarsa, maimakon kwana 60 da ake bayarwa a baya.
- Za a riƙa sake tantance ɗaliban ƙasashen waje akai-akai domin tabbatar da bin ƙa'idojin biza.
Sakataren Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida ya bayyana cewa tsarin da ake amfani da shi a baya ya bai wa wasu damar ci gaba da zama a Amurka ta hanyar ci gaba da yin rajistar sabbin kwasa-kwasai, ba tare da wata iyaka ba.
Sai dai ƙungiyoyin da ke ba jami'o'i shawara kan harkokin ɗaliban ƙasashen waje sun nuna rashin amincewa da matakin, suna mai cewa sabbin ƙa'idojin na iya janyo ƙalubale ga ɗalibai da cibiyoyin ilimi, musamman ga waɗanda shirye-shiryen karatunsu ke ɗaukar fiye da shekara huɗu, kamar digiri na biyu da na digirgir.