Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD), Antonio Guterres, ya bayyana cewa bai dace a kai hare-hare kan gine-ginen fararen hula ba, yayin da rikicin tsakanin Iran da Amurka ke ci gaba da ƙamari.
Iran ta zargi Amurka da kai hare-hare kan wasu gadoji da cibiyoyin sufuri a ƙasar, zargin da har yanzu Amurka ba ta tabbatar da shi ba.
Mai magana da yawun Sakatare Janar na MDD, Farhan Haq, ya shaida wa manema labarai cewa Antonio Guterres na ci gaba da nuna matuƙar damuwa kan yadda rikicin ke ƙara ta'azzara, yana mai kira ga ɓangarorin da su kauce wa matakan da za su ƙara rura wutar rikici.
A cewarsa, Sakatare Janar ɗin ya fi nuna damuwa musamman kan hare-haren da ake kai wa gine-ginen fararen hula a Iran da sauran sassan yankin.
"Kai hare-hare kan gine-ginen fararen hula ba abin da za a amince da shi ba," in ji Farhan Haq.
Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan labari, Amurka ba ta tabbatar da iƙirarin Iran na cewa ta kai hare-hare kan cibiyoyin fararen hula ba. MDD ta kuma sake jaddada kiranta ga dukkan ɓangarorin da su mutunta dokokin jin ƙai na ƙasa da ƙasa tare da kare rayukan fararen hula.