Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa tana nazarin yiwuwar gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na gwaji kafin babban zaɓen shekarar 2027, domin gwada inganci da sahihancin na'urori da sauran kayayyakin zaɓe.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan (SAN), ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake karɓar baƙuncin Jakadan Birtaniya a Najeriya, Dr. Richard Montgomery, a hedikwatar INEC da ke Abuja, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.
A cewarsa, matakin na daga cikin ƙoƙarin hukumar na inganta tsarin gudanar da zaɓe, musamman bayan ƙorafe-ƙorafen da suka biyo bayan babban zaɓen shekarar 2023.
"Muna nazarin yiwuwar gwada duka kayayyaki da na'urorin zaɓenmu kafin babban zaɓen da ke tafe, ciki har da yiwuwar gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na gwaji domin tabbatar da ingancinsu," in ji Farfesa Amupitan.
Ya ƙara da cewa shirin zai taimaka wajen tantance yadda fasahohin da hukumar ke amfani da su ke aiki, tare da gano matsalolin da za a iya gyarawa kafin gudanar da babban zaɓe.
Shugaban INEC ya kuma ce hukumar na ci gaba da bunƙasa tsarin tantance masu zaɓe ta hanyar na'ura, da amfani da shafin IReV wajen tura sakamakon zaɓe, da kuma ƙarfafa tsaron tsarin bayanan hukumar domin ƙara inganta sahihanci da amincewar jama'a ga tsarin zaɓen.