Takaddama ta ɓarke tsakanin Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab'i ta Jihar Kano kan ikon da ya shafi sana'ar tura fina-finai, wato downloading.

Tun da farko, Hukumar Hisbah ta sanar da haramta sana'ar, tana mai zargin cewa wasu na amfani da ita wajen yaɗa fina-finan batsa da sauran abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya da al'adun al'umma.

Sai dai Hukumar Tace Fina-finai ta yi watsi da matakin, tana mai cewa sana'ar halastacciya ce, kuma ita ce doka ta bai wa ikon tsara da kuma sa ido kan masu gudanar da ita.

Kakakin hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya ce irin wannan mataki ya kamata a tattauna a tsakanin hukumomin biyu kafin a aiwatar da shi.

"Mu ne doka ta ba hurumin kula da masu wannan sana'a. Ya kamata a zauna a tattauna kafin a ɗauki irin wannan mataki," in ji shi.

Ya ƙara da cewa hukumar ta riga ta samar da ƙa'idojin da ke hana masu sana'ar yaɗa fina-finai ba tare da izinin masu haƙƙin mallaka ba, domin rage rikice-rikicen da ke tsakaninsu da masu shirya fina-finai.

A nata ɓangaren, Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Dakta Mujahid Aminuddeen, ya ce matakin ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafe da dama daga al'umma.

A cewarsa, wasu mutane na amfani da sana'ar wajen yaɗa hotuna da bidiyoyin tsiraici da kuma fina-finan batsa, abin da ya ce na lalata tarbiyya da ɗabi'un al'umma.

"Akwai wasu ɓata-gari da ke fakewa da wannan sana'a suna yaɗa fina-finan batsa da sauran abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya," in ji Dakta Mujahid.

Takaddamar ta sake jawo hankalin jama'a kan batun iyakokin ikon hukumomi da kuma yadda za a daidaita kula da harkokin masana'antar fina-finai tare da kare tarbiyyar al'umma.