Mai bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan yaɗa labarai, Daniel Bwala, ya ce dakarun sojin Nijeriya sun kama wasu baƙin haure da ake zargi da hannu a matsalolin tsaro da ke addabar wasu sassan ƙasar.
Bwala ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da aka wallafa ranar Juma’a, inda ya ce gwamnati ta zaɓi kada ta bayyana ƙasashen da waɗanda aka kama suka fito saboda ana ci gaba da tattaunawar diflomasiyya da ƙasashen da abin ya shafa.
A cewarsa, ɓoye bayanan waɗanda aka kama wani mataki ne da aka ɗauka domin kauce wa duk wani cikas ga hulɗar diflomasiyya tsakanin Nijeriya da ƙasashen da ake zargin mutanen suka fito.
Ya ƙara da cewa, a wasu lokuta ana tsare irin waɗannan mutane har sai an cimma yarjejeniya tsakanin ƙasashe, wanda kan haɗa da musayar fursunoni idan hakan ya zama wajibi.
Bwala ya kuma danganta wasu daga cikin tsoma bakin ƙasashen waje cikin harkokin tsaron Nijeriya da muradun tattalin arziki da na tsaro. Ya tuna da yadda aka riƙa daga tutocin Rasha a wasu zanga-zanga da aka gudanar a Arewacin ƙasar, yana mai cewa irin waɗannan abubuwa na iya nuna tasirin ƙasashen waje.
Da aka tambaye shi ko Hukumar Leken Asirin Amurka (CIA) na da hannu wajen ɗaukar nauyin ta’addanci a Nijeriya, Bwala ya ce ba zai iya tabbatar da hakan ba.
Sai dai ya ce wani ɗan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya taɓa yin irin wannan zargi a yayin wani zaman sauraron ra’ayoyi a Majalisar Dokokin Amurka.
Bwala ya kuma bayyana cewa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP sun bazu daga yankin Arewa maso Gabas zuwa Arewa maso Yamma, tare da ƙoƙarin kutsawa yankin Arewa ta Tsakiya, yana mai cewa gwamnati na ɗaukar matakan da suka dace domin dakile ci gaban su.
Ya musanta zargin da ake yi cewa sojojin Nijeriya na kare ‘yan ta’adda, amma ya amince cewa akwai yiwuwar samun masu ba da bayanan sirri daga cikin jami’an tsaro, abin da ya ce hukumomi ke ƙoƙarin magancewa.
A ƙarshe, Bwala ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta inganta haɗin kai tsakanin Sojojin Ƙasa da Sojojin Sama, tare da bayyana cewa an samu ci gaba a fannonin tsaro da tattalin arzikin ƙasar.