Babbar Kotun Tarayya da ke Minna, Jihar Neja, ta yi watsi da wata buƙata da aka gabatar domin sauya sunayen ɓangarorin da ke cikin ƙarar da ke ƙalubalantar zaɓen fidda gwani na jam'iyyar APC a mazaɓar Magama/Rijau.
Ƙarar ta samu ne daga ɗan takarar APC, Shehu Auna, ta hannun lauyansa, Abubakar Danjuma, wanda ke ƙalubalantar sahihancin zaɓen fidda gwani da aka gudanar a ranar 16 ga Yunin 2026, wanda ya tsayar da Yakubu Auna a matsayin ɗan takarar jam'iyyar.
A hukuncin da ya yanke, Mai Shari'a Abdullahi Aminu Dan-Ige ya ce masu ƙarar sun kasa gabatar da hujjojin da za su gamsar da kotu ta amince da buƙatar sauya sunayen ɓangarorin da ke cikin shari'ar, saboda haka ya yi watsi da ita.
Sai dai lauyan mai ƙarar ya bayyana cewa hukuncin bai shafi ainihin ƙarar da ke ƙalubalantar sahihancin zaɓen fidda gwanin APC ba.
Kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari'ar zuwa 22 ga Yulin 2026.