Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai na Kenya sun ce wasu masu kutse ta intanet sun kutsa cikin shafin intanet na fadar shugaban ƙasar, William Ruto, tare da neman a biya su bitcoin biyar, wanda darajarsa ta kai kusan Shilling miliyan 41 na Kenya (kimanin dala 320,000) kafin su saki shafin.

A cewar rahotannin, masu kutse sun sauya shafin farko na intanet, inda suka maye gurbin bayanan hukuma da saƙonnin cin mutunci ga shugaban ƙasar, tare da barazanar fitar da wasu muhimman bayanan gwamnati.

A halin yanzu, shafin president.go.ke ba ya aiki, kuma yana nuna saƙon cewa ana gudanar da gyare-gyare, tare da alƙawarin dawo da shi cikin ƙanƙanin lokaci.

Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan labari, hukumomin Kenya ba su fitar da wata sanarwa a hukumance da ke tabbatar ko musanta rahotannin kutse ba.

Lamarin ya zo ne watanni kaɗan bayan wani babban harin kutse da ya shafi wasu shafukan intanet na gwamnatin Kenya a watan Nuwamban 2025, wanda hukumomi suka bayyana a lokacin a matsayin hari da aka shirya tare da haɗin gwiwa.