Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Whirl Stroke, tare da haɗin gwiwar jami'an tsaron al'umma na Jihar Benue, sun kashe wasu da ake zargin 'yan ta'adda biyu, tare da ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Katsina-Ala ta jihar.

A cikin wata sanarwa, rundunar ta bayyana cewa an gudanar da samamen ne da misalin karfe 3:00 na safiyar ranar 16 ga Yulin 2026, bayan samun bayanan sirri kan inda waɗanda ake zargin ke buya.

Sanarwar ta ce dakarun sun bi ta Takum a Jihar Taraba zuwa ƙauyukan Tse Togo da Utenge, kusa da sansanin Orter, inda aka ce waɗanda ake zargin 'yan ta'addan ke fakewa.

"A yayin musayar wuta, dakarun sun samu nasarar kashe mutum biyu daga cikin waɗanda ake zargin 'yan ta'addan ne," in ji sanarwar.

Rundunar ta ce mutanen uku da aka ceto duk mazauna ƙaramar hukumar Katsina-Ala ne, yayin da wasu daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su suka yi amfani da damar artabun wajen tserewa daga sansanin.

Hakazalika, sojojin sun ce sun ƙwato makamai, harsasai da wasu kayan aikin soja a yayin gudanar da samamen.

Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan labari, rundunar ba ta bayyana cikakken adadin mutanen da suka tsere daga sansanin ko kuma ko an kama wasu da ake zargi da hannu a lamarin ba.