Shugaban ƙasar Lebanon, Joseph Aoun, ya bar birnin Beirut zuwa Washington, inda ake sa ran zai gana da shugaban Amurka, Donald Trump, kamar yadda fadar shugaban ƙasar ta sanar.
Ziyarar ta zo ne bayan kammala zagaye na shida na tattaunawar Lebanon da Isra'ila, wanda aka gudanar a ofishin jakadancin Amurka da ke Rome, ƙasar Italiya, a ranakun 13 da 14 ga watan Yuli.
A cewar fadar shugaban ƙasar Lebanon, Aoun zai tattauna da manyan jami'an gwamnatin Amurka kan halin tsaro da siyasar ƙasarsa, da kuma hanyoyin ƙarfafa yarjejeniyar tsagaita wuta, musamman a kudancin Lebanon.
Ana kuma sa ran tattaunawar za ta mayar da hankali kan batun janye sojojin Isra'ila daga wuraren da har yanzu suke mamaye a Lebanon, wanda ke ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan batutuwan da ke gaban ɓangarorin biyu.
Haka kuma, ana sa ran bangarorin za su tattauna kan hanyoyin ƙarfafa zaman lafiya da rage tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.