Ana ci gaba da tattaunawa a Najeriya kan shirin kafa rundunar ƴansandan jihohi, bayan da Majalisar Dokokin Tarayya ta amince da ƙudurin dokar a karatu na biyu.

Majalisar ta zaɓi amfani da ƙudurin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar, maimakon wasu ƙudurorin da ƴan majalisa suka gabatar tun da farko.

Buƙatar kafa ƴansandan jihohi ta daɗe tana cikin manyan buƙatun gwamnonin jihohi, waɗanda ke cewa rashin ikon kafa rundunar ƴansandan jiha na hana su ɗaukar matakan da suka dace wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar yankunansu.

Kafin wannan yunƙuri, jihohi da dama sun riga sun kafa rundunonin tsaro na cikin gida, irin su ƴan sa-kai, ƴan banga da kuma askarawa, domin tallafa wa jami'an tsaron ƙasa wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Sai dai shirin na ci gaba da haifar da ra'ayoyi mabambanta. Wasu na ganin kafa ƴansandan jihohi zai taimaka wajen inganta tsaro saboda sun fi sanin yankunansu, yayin da wasu ke nuna fargabar cewa za a iya amfani da rundunar wajen cimma muradun siyasa ko kuma ta fuskanci irin matsalolin da ake zargin wasu rundunonin tsaro na cikin gida da su, ciki har da cin zarafin jama'a da rashin ƙwarewa.

Ana sa ran ci gaba da tattaunawa kan ƙudurin a majalisa kafin a yanke hukunci na ƙarshe kan dokar.