Hukumomi a arewacin Mali sun ce mayaƙan Tuareg masu neman ɓallewa tare da mayaƙan ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi sun kashe aƙalla sojojin Mali 50 a wani kwanton-ɓauna da suka yi wa ayarin motocin soji a ranar Asabar.

A cewar jami'an yankin, maharan sun kuma yi garkuwa da sama da mutum 20 a yayin harin.

Bayanin ya zo daidai da iƙirarin da Azawad Liberation Front (FLA) ta yi, inda ta ce mayaƙanta sun yi wa sojojin Mali da kuma dakarun Rasha da ke mara musu baya mummunar illa a harin.

A cewar FLA, ayarin motocin sojin na kan hanyarsa ne daga garin Anefis, mai muhimmanci ta fuskar dabarun soja, zuwa birnin Gao, lokacin da mayaƙan suka kai musu harin.

Sai dai har zuwa yanzu, gwamnatin Mali ba ta fitar da cikakken bayani a hukumance kan adadin waɗanda suka mutu ko kuma halin da ake ciki bayan harin.