Ana sa ran shugaban Amurka, Donald Trump, zai halarci wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya tsakanin Spain da Argentina a ranar Lahadi, inda ake sa ran zai miƙa kofin ga tawagar da za ta lashe gasar tare da shugaban FIFA, Gianni Infantino.
Ziyarar Trump na zuwa ne bayan ce-ce-ku-ce da ya janyo sakamakon wani rahoto da ya ce ya kira shugaban FIFA kai tsaye domin neman a ɗage dakatarwar ɗan wasan Amurka, Folarin Balogun, kafin wasan zagaye na 16.
Rahoton ya haifar da muhawara da suka daga wasu ɓangarori, waɗanda suka nuna damuwa kan yiwuwar tsoma bakin siyasa a harkokin ƙwallon ƙafa da FIFA ke gudanarwa.
Sai dai Trump ya bayyana cewa Gasar Kofin Duniya ta 2026 na ɗaya daga cikin gasannin da suka fi samun nasara a tarihi, yana mai cewa ta ƙara bunƙasa da kuma yaɗa farin jinin wasan ƙwallon ƙafa a Amurka.
Har zuwa yanzu, FIFA ba ta fitar da wata sanarwa da ke tabbatar da rahoton cewa an nemi a sauya hukuncin dakatar da ɗan wasan ba.