Hukumar agajin gaggawa ta Red Crescent a Iran ta ce wata girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 5.0 a ma'aunin Richter ta afku a yankin Saland da ke lardin Khuzestan da safiyar Lahadi.

Babban Daraktan Hukumar a lardin ya bayyana cewa girgizar ƙasar ta auku ne da misalin karfe 5:55 na safiya, yayin da cibiyarta ke da zurfin kilomita 12 ƙarƙashin ƙasa.

A cewarsa, an tura tawagogin ceto guda biyu zuwa ƙauyukan da ke kusa da inda girgizar ta afku domin tantance ko an samu ɓarna ko asarar rayuka.

Hakazalika, an sanya dukkan cibiyoyin Red Crescent da ke lardin Khuzestan cikin shirin ko-ta-kwana domin ba da agajin gaggawa idan buƙatar hakan ta taso.

Har zuwa lokacin wallafa wannan labari, babu wani rahoto da ke nuna an samu asarar rayuka ko wata babbar ɓarna sakamakon girgizar ƙasar, yayin da hukumomi ke ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki.