SERAP ta bukaci Majalisar Dokoki ta Kasa da ta janye kudirin gyaran Dokar Kare Bayanai ta Najeriya na 2026, tana mai cewa wata hanya ce ta bayan fage da gwamnati ke son amfani da ita wajen sanya ido da takaita 'yancin bayyana ra'ayi a kafafen sada zumunta.
SERAP ta yi gargadin cewa za ta shigar da kara a kotu idan aka zartar da kudirin dokar a yadda yake yanzu ko kuma da wani salo mai kama da shi.
Kudirin dokar, wanda Sanata Ned Nwoko (APC, Delta North) ya dauki nauyin gabatarwa, na neman tilasta wa kafafen sada zumunta, masu sarrafa bayanai (data controllers) da masu aiwatar da sarrafa bayanai (data processors) da ke aiki a Najeriya su bude ofisoshi na zahiri a cikin kasar.
Haka kuma, kudirin ya bai wa Hukumar Kare Bayanai ta Najeriya (Nigeria Data Protection Commission - NDPC) ikon dakatar da ko haramta ayyukan duk wata hukuma ko kamfani da ya kasa bin tanade-tanaden dokar cikin kwanaki 30.