Kwamitin gudanar da zaɓen Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (ECNBA) ya ayyana Oyinkansola Badejo-Okusanya a matsayin shugabar Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta 33 bayan ta lashe zaɓen ƙungiyar.


Shugaban kwamitin zaɓen, Aham Ejelam, ya bayyana a Abuja cewa Badejo-Okusanya ta samu ƙuri'u 12,317 (kashi 47.18%), inda ta doke babban abokin hamayyarta Lateef Akangbe, wanda ya samu ƙuri'u 7,934 (kashi 30.39%). Sai kuma Olumuyiwa Akinboro da ya zo na uku da ƙuri'u 5,855.


A cewar ECNBA, mutum 26,106 ne suka kaɗa ƙuri'a daga cikin masu rajista 82,172, wanda ya nuna kashi 31.86% na masu zaɓe.


Haka kuma, an zaɓi Oghenero Okoro a matsayin mataimakiyar shugaba ta farko, Afam Okeke a matsayin babban sakatare, Aghogho Gladys a matsayin mataimakiyar babban sakatare, da Chinelo Ofoegbunam a matsayin sakatariyar walwala.


Da yake jawabi bayan sanar da sakamakon, shugaban NBA mai barin gado, Afam Osigwe, ya ce zaɓen ya fuskanci yunƙurin kawo cikas, ciki har da harin yanar gizo (cyberattack), amma kwamitin ya shawo kan matsalolin tare da matsar da tsarin gudanar da zaɓen zuwa sabar da ta fi tsaro.


Osigwe ya buƙaci waɗanda suka yi nasara su nuna dattako, yayin da ya roƙi waɗanda suka sha kaye su haɗa kai da sabon shugabancin domin ci gaban ƙungiyar. Ya kuma ce za a gudanar da cikakken nazari kan ƙalubalen da aka fuskanta domin inganta tsaron bayanai da tsarin zaɓen NBA a nan gaba.