Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta daƙile wani hari da mayaƙan ƙungiyar ISWAP suka kai kan wani sansanin soji da ke ƙauyen Logomani a ƙaramar hukumar Ngala ta Jihar Borno.
A cewar rahoton kafar yaɗa labarai ta Daily Post, kakakin rundunar Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya bayyana cewa maharan sun samu damar mamaye wani ɓangare na sansanin na ɗan lokaci kafin dakarun sojin su sake tsara kansu tare da ƙaddamar da farmakin martani.
Ya ce a yayin artabun, an kashe wasu daga cikin mayaƙan ISWAP, sai dai soja guda ɗaya ya rasa ransa.
"Abin takaici, soja ɗaya ya sadaukar da rayuwarsa a yayin artabun, yayin da aka lalata motocin yaƙi guda biyu da kuma wasu kayan aikin soja," in ji Kyaftin Goni.
Kakakin rundunar bai bayyana takamaiman ranar da harin ya faru ba, haka kuma rahoton Daily Post bai fayyace hakan ba. Sai dai ya ce an shawo kan lamarin bayan an tura ƙarin dakaru domin ƙarfafa tsaron yankin.
A wani ci gaba kuma, rundunar ta tunatar da cewa a ranar 12 ga watan Yuli, ta daƙile wani hari da ISWAP ta kai kan wani sansanin soji a ƙaramar hukumar Kukawa ta Jihar Borno, inda ta kuma kama wani da ake zargin ɗan ƙasar Morocco ne.
Hakazalika, rundunar ta ce a wani samame daban da ta kai a ƙaramar hukumar Askira/Uba, ta ceto mutum biyu da aka yi garkuwa da su, tare da ƙwace kuɗi kimanin dala 870 na Amurka da kuma wasu kayan abinci.