Hukumomi a ƙasar Guyana sun ce wani jirgin ruwa da ke ɗauke da fasinja 116 ya nutse a gabar Tekun Atlantika, inda kawo yanzu aka ceto mutum takwas kacal.
Ministan Ayyukan Jama'a na ƙasar, Juan Edghill, ya bayyana cewa jirgin na kan hanyarsa ne daga babban birnin ƙasar, Georgetown, zuwa Port Kaituma da ke arewacin Guyana lokacin da hatsarin ya faru a daren Asabar.
A cewarsa, jami'an agaji da masu ceto na ci gaba da gudanar da aikin neman da ceto domin gano sauran fasinjojin da ke cikin jirgin.
Har zuwa lokacin wallafa wannan labari, hukumomi ba su bayyana musabbabin hatsarin ba, yayin da bincike ke ci gaba domin gano abin da ya haddasa nutsewar jirgin.