Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya karɓi ragamar shugabancin Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), a daidai lokacin da ƙungiyar ke fuskantar manyan ƙalubale da suka haɗa da ficewar wasu ƙasashe daga cikinta da kuma matsalolin siyasa da tattalin arziki.
An zaɓi Faye ne a matsayin sabon shugaban ƙungiyar yayin taron shugabannin ƙasashe da gwamnatocin ECOWAS da aka gudanar a Freetown, babban birnin Saliyo.
A yayin taron, shugabannin ƙasashen ECOWAS sun kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar gina bututun iskar gas da zai haɗa Najeriya da Morocco, wanda ake sa ran zai kasance mai tsawon kusan kilomita 6,000.
Bututun zai ratsa wasu ƙasashe 13 da ke gabar Tekun Atlantika, inda zai ɗauki iskar gas daga Najeriya zuwa Morocco, daga nan kuma a tura shi zuwa kasuwannin Turai ta hanyar bututun yankin Maghreb.
Shugaban Saliyo kuma tsohon shugaban ECOWAS, Julius Maada Bio, ne ya tabbatar da cimma yarjejeniyar, wadda ake sa ran za ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziki da makamashi tsakanin ƙasashen Yammacin Afirka.