Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation HADIN KAI sun kama wani mutum ɗan ƙasar Sudan mai suna Musa Fashir, mai shekaru 32, wanda ake zargi da kasancewa mayaƙin ta'addanci na ƙasashen waje.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce an kama shi ne a wani samame da aka kai a yankin Lassa da ke ƙaramar hukumar Askira/Uba a jihar Borno a ranar 19 ga Yulin 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri.
Rundunar ta bayyana cewa wanda ake zargin na da alaƙa da wasu ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya, lamarin da ke nuna yiwuwar samun goyon baya daga wasu 'yan ƙasashen waje ga ayyukan ta'addanci a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Haka kuma, sojojin sun kama wata mata mai suna Mary Florence, mai shekaru 36, wadda ta bayyana kanta a matsayin 'yar ƙasar Ghana, inda ake zargin ta shiga Najeriya ba bisa ƙa'ida ba.
Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin tantance yadda ta shiga yankin, sahihancin bayanan da ta bayar, da kuma yiwuwar alaƙarta da ayyukan ta'addanci ko wasu laifukan ƙetare.
A cewar rundunar, mutanen biyu na ci gaba da kasancewa a tsare yayin da bincike ke gudana.