'Yan sandan lardin Sistan da Baluchistan na Iran sun sanar da cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe Malam Maulvi Mohammad Anwar Rigi, limamin Juma'a na Sunni a garin Mirjaveh.

A cikin wata sanarwa da rundunar 'yan sandan ta fitar, ta ce maharan sun harbe malamin ne da safiyar Litinin sannan suka tsere daga wurin da abin ya faru.

Sanarwar ta ce jami’an tsaro da na agajin gaggawa sun isa wurin da harin ya faru, kusa da Babban Masallacin Mirjaveh, domin kai ɗauki.

Sai dai duk da ƙoƙarin da likitoci suka yi na ceton rayuwarsa, Maulvi Mohammad Anwar Rigi ya rasu sakamakon munanan raunukan da ya samu.

Hukumomin Iran sun ce sun fara bincike domin gano waɗanda suka aikata harin da kuma dalilan da suka haifar da kashe malamin.