Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Borno, Usman Tar, ya tabbatar da cewa ɗalibai uku sun mutu yayin musayar wuta tsakanin dakarun sojin Najeriya da mayaƙan ƙungiyar ISWAP bayan harin da suka kai garin Monguno da ke jihar Borno.

A tattaunawarsa da BBC, kwamishinan ya ce mayaƙan ISWAP sun kai harin ne da nufin yin garkuwa da ɗaliban makarantar sakandaren ƴan mata ta Federal Government Girls College (FGGC) da ke Monguno.

Ya bayyana cewa yayin da sojoji ke artabu da maharan domin dakile harin, wasu harsasai sun samu ɗalibai, lamarin da ya yi sanadin mutuwar uku daga cikinsu, yayin da wasu kuma suka jikkata.

Tun da farko, Rundunar Operation HADIN KAI ta sanar cewa maharan sun kai farmaki makarantar da misalin ƙarfe 1:30 na safiyar ranar 19 ga Yuli, amma jami'an tsaro da ke gadin makarantar tare da goyon bayan jami'an MOPOL da dakarun gaggawa sun yi nasarar fatattakar su.

Rundunar ta ƙara da cewa an ceto ɗalibai 46 tare da kwashe su zuwa Barikin Kinnasara da ke Monguno domin duba lafiyarsu, kuma babu wani ɗalibi da aka yi garkuwa da shi.

Haka kuma ta ce ana ci gaba da farautar maharan da kuma binciken mutanen da ake zargin sun taimaka musu wajen kai harin, tare da miƙa ta'aziyya ga iyalan ɗaliban da suka rasu.