Rundunar Sojin Amurka ta Tsakiya (CENTCOM) ta sanar da cewa sojojinta uku sun mutu cikin kwanaki biyu sakamakon hare-haren da ake dangantawa da Iran, yayin da rikicin tsakanin ƙasashen biyu ke ci gaba da ta'azzara.
A cewar rundunar, sojoji biyu sun mutu bayan wani hari da aka kai kan sansanin sojin Amurka da ke Jordan a ranar Juma'a, yayin da har yanzu ake neman wani soja guda ɗaya da ya ɓace.
Haka kuma, wani soja na uku ya rasu a arewacin Iraki a ranar Asabar yayin wani hari da CENTCOM ta danganta da Iran.
Rundunar ta bayyana cewa sojan da ya mutu a Iraki ya rasa ransa ne yayin wani aiki na lalata ragowar wani jirgin yaƙi mara matuƙi (drone) na Iran da aka harbo, yayin da wani soja guda ɗaya ya samu raunuka a wannan harin.
A wani sabon bayani, CENTCOM ta ce an gano wasu gawarwaki da ba a tantance ko su waye ba a wurin harin da aka kai a Jordan, kuma ana ci gaba da bincike domin gano asalinsu.
Wannan na zuwa ne yayin da Amurka da Iran ke ci gaba da musayar hare-hare a rana ta takwas a jere.
Sai dai, har yanzu ba a samu wata sanarwa daga Iran da ta tabbatar ko ta musanta alhakin hare-haren da CENTCOM ta danganta da ita ba.