Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta sake jaddada ƙudurinta na ƙaddamar da kuɗin bai ɗaya na yankin, ECO, a shekarar 2027, tana mai bayyana hakan a matsayin wani babban mataki na ƙara haɗa tattalin arziƙin ƙasashen yankin, ƙarfafa kasuwancin cikin gida da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa a faɗin Yammacin Afirka.


An cimma wannan matsaya ne a zaman taro na 69 na Shugabannin Ƙasashe da Gwamnatocin ECOWAS, wanda aka gudanar ranar Lahadi a birnin Lungi na ƙasar Saliyo, ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙasar, Julius Maada Bio.


A cikin sanarwar ƙarshe da aka fitar ranar Talata bayan kammala taron, shugabannin sun bayyana cewa tattalin arziƙin ƙasashen ECOWAS ya ci gaba da nuna juriya duk da ƙalubalen tattalin arziƙin duniya. Sun kuma yi hasashen cewa shekarar 2026 za ta kasance mai kyau ga tattalin arziƙin yankin, sakamakon raguwar hauhawar farashi, raguwar yawan bashin gwamnati idan aka kwatanta da girman tattalin arziƙi (GDP), da kuma ƙaruwa a gibin rarar kuɗaɗen shigar da fitar da kayayyaki. Sai dai sun nuna damuwa kan ci gaba da kasancewar gibin kasafin kuɗi.


Game da shirin ƙaddamar da kuɗin bai ɗaya, shugabannin ECOWAS sun bayyana cewa.


Hukumar ta sake jaddada cikakken ƙudurinta na ƙaddamar da kuɗin ECO a shekarar 2027, a matsayin muhimmin kayan aiki na ƙara haɗa tattalin arziƙin yankin da kuma bunƙasa ci gaba mai ɗorewa, mai haɗa kowa da kowa, kuma mai juriya a tsakanin ƙasashen mambobin ƙungiyar.