Kwamishinan 'Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya (FCT), CP Ahmed Sanusi, ya bukaci mazauna yankin, musamman matasa, da kada su bari jami'an 'yan sanda su binciki wayoyinsu na hannu yayin ayyukan tsayawa da bincike (stop-and-search), yana mai cewa hakan ya saba da umarnin Sufeto Janar na 'Yan Sanda (IGP).


Sanusi ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da News Central Television ta wallafa a ranar Talata, inda ya sake jaddada cewa an haramta wa jami'an 'yan sanda binciken wayoyin jama'a ba tare da wani dalili na doka ba.


Ya ce, "An riga an fayyace batun binciken waya. Saboda yadda wasu jami'ai da ma'aikata ke amfani da wannan dama wajen cin zarafi da karɓar rashawa, ba kawai a cikin rundunar 'yan sanda ba har ma da wasu hukumomin tsaro, an bayar da umarni cewa babu wanda ya isa ya binciki wayar wani."


Kwamishinan ya bayyana cewa duk da cewa wayoyin hannu na iya zama hujja a binciken laifuka, amma ya kamata a bincike su ne kawai bayan an kama wanda ake zargi bisa doka sannan aka kai shi ofishin 'yan sanda domin ci gaba da bincike.