Jami’an Sashen Yaƙi da Garkuwa da Mutane na Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja sun kama wani mutum mai suna Umaru Danda, bisa zargin samar da miyagun ƙwayoyi da sauran kayan aiki ga masu garkuwa da mutane da ke gudanar da ayyukansu a Abuja.


Kwamishinan ’yan sandan Abuja, Ahmed Mohammed Sanusi, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar ranar Litinin.


Ya ce kama wanda ake zargin ya biyo bayan binciken da rundunar ta gudanar kan wani lamari na garkuwa da mutane da ya faru a yankin Yellow House da ke Mpape a ranar 8 ga Yuli, 2026. Bayan samun bayanan sirri, jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane sun bi diddigin wanda ake zargin tare da cafke shi a ranar 10 ga Yuli.


Kwamishinan ya ce bincike ya nuna cewa ƙungiyar masu garkuwa da mutanen da suka kai harin Mpape na samun miyagun ƙwayoyi da sauran kayan aiki daga hannun Danda, waɗanda ake zargin yana samar musu domin ci gaba da ayyukansu na ta’addanci.


Ya ce bayan kama shi, wanda ake zargin ya jagoranci jami’an ’yan sanda zuwa maboyar ƙungiyar guda uku a Jihar Neja, inda aka kwato kayayyaki da suka haɗa da allunan tramadol, abubuwan da ake zargin hodar iblis ne, ƙwayoyin tabar wiwi da sauran miyagun ƙwayoyi.


Haka kuma, jami’an sun kwato wasu buhuna masu ɗauke da busasshen ganyen da ake zargin tabar wiwi ne, ma’aunin dijital, katunan banki guda biyu, kuɗi Naira 250,000 da kuma bindigar AK-47.


Rundunar ta ce wanda ake zargin da kayayyakin da aka kwato suna hannun ’yan sanda, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.


A wani labarin makamancin haka, kwamishinan ya ce jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane sun yi nasarar ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi a yankin Karshi da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.