Dakarun Operation HADIN KAI sun dakile wani yunkuri na 'yan ta'addan Boko Haram/Islamic State West Africa Province (ISWAP) na karɓar haraji ba bisa ka'ida ba a Jihar Yobe, inda suka kashe ɗan ta'adda guda tare da ƙwace makamai, alburusai da kayayyakin aiki.


Samamen da dakarun Sashe na 2 na Operation HADIN KAI suka gudanar ya kuma tarwatsa wani yunkuri da ake zargin 'yan ta'addan na yi na karɓar haraji ba bisa ka'ida ba daga mazauna yankin, lamarin da ya katse wata hanya da ake zargin suna amfani da ita wajen samun kuɗaɗen gudanar da ayyukansu.


Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mukaddashin Jami'in Yaɗa Labaran Soja na Hedikwatar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation HADIN KAI a Arewa maso Gabas, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar ranar Talata.


Sanarwar ta ce, "Bayan samun sahihan bayanan sirri kan motsin motoci kirar Volkswagen Golf guda biyu da babura da ake zargin suna ɗauke da 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP domin karɓar haraji ba bisa ka'ida ba daga al'ummomin yankin, dakarun Forward Operating Base (FOB) Bukarti, tare da haɗin gwiwar 27 Task Force Brigade, sun gaggauta fita sintirin farmaki zuwa yankin Paya Kafiya da misalin ranar 19 ga Yulin 2026."