Tsohon fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Faransa, Zinedine Zidane, ya rattaba hannu kan yarjejeniya domin zama sabon mai horas da tawagar ƙasar Faransa.
Rahotanni sun bayyana cewa Zidane zai jagoranci Les Bleus har zuwa shekarar 2030, inda zai karɓi ragamar horar da tawagar daga Didier Deschamps, wanda ya shafe shekaru 14 yana jagorantar ƙungiyar.
Deschamps ya jagoranci Faransa tun shekarar 2012, inda ya lashe Kofin Duniya na 2018 tare da kai tawagar wasan ƙarshe a gasar 2022 da kuma 2026.
Zidane kuwa ya yi fice a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ’yan wasan Faransa a tarihi, inda ya taimaka wa ƙasarsa lashe Kofin Duniya na 1998 da kuma Gasar Cin Kofin Nahiyar Turai ta Euro 2000.
A fannin horarwa kuma, ya kafa tarihi ne tare da Real Madrid bayan jagorantar ƙungiyar zuwa lashe gasar UEFA Champions League sau uku a jere tsakanin 2016 da 2018.
Naɗin Zidane na zuwa ne da babban buri daga magoya bayan ƙwallon ƙafa na Faransa, waɗanda ke fatan zai ci gaba da gina nasarorin da tawagar ta samu a shekarun baya tare da jagorantar ta zuwa ƙarin kofuna a manyan gasannin duniya.