Amurka ta zuba jarin dala miliyan 1.2 cikin shekaru biyar da suka gabata domin tallafa wa ayyukan kare da adana al'adun gargajiya a jihohi 21 na Najeriya, inda ta bayyana wannan shiri a matsayin wata dabarar zuba jari da ke amfanar da Najeriya da kuma Amurka baki ɗaya.
Mukaddashin Jakadan Amurka a Najeriya, Keith Heffern, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin ƙaddamar da wani aikin kare al'adun gargajiya da Gidauniyar Wheyham Foundation ta gudanar a Abuja.
Ya ce an samar da wannan tallafi ne galibi ta hanyar Asusun Jakadun Amurka na Kare Al'adun Gargajiya (Ambassadors Fund for Cultural Preservation), kuma hakan ya taimaka wajen adana al'adun Najeriya tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.
Ya ce, "A cikin shekaru biyar da suka gabata kaɗai, Amurka ta zuba dala miliyan 1.2 wajen ayyukan kare al'adun gargajiya a jihohi 21 na Najeriya, galibi ta hanyar Asusun Jakadun Amurka na Kare Al'adun Gargajiya. Ba tallafi kawai ba ne, illa wata dabarar zuba jari ce da ke ciyar da muradun Amurka gaba tare da amfanar Najeriya."
A cewarsa, sakamakon wannan aikin ya haɗa da adana fiye da kayan tarihi na Nok guda 250 ta hanyar fasahar zamani, inganta wani gidan adana kayan tarihi, horar da matasa 'yan Najeriya 50 kan ƙwarewar fasahar zamani, tare da kai wa fiye da mutane 50,000 a faɗin ƙasar.
Ya ƙara da cewa, "Sakamakon ya bayyana a fili: an adana fiye da kayan tarihin Nok guda 250 ta hanyar fasahar dijital, an inganta gidan adana kayan tarihi gaba ɗaya, an horas da matasa 'yan Najeriya 50 kan sabbin ƙwarewar fasahar dijital, sannan an kai wa sama da mutane 50,000 a faɗin ƙasar. An gina wannan dandali ne galibi da fasahar Amurka, wanda ya samar da ingantaccen zuba jari, sakamako mai auna inganci da tasiri mai ɗorewa. Wannan shi ne ainihin yadda haɗin gwiwar Amurka wajen kare al'adun gargajiya yake."