Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun daƙile wani yunƙuri da mayaƙan Boko Haram/ISWAP suka yi na tatsar kuɗi daga al'ummomi a Jihar Yobe ta hanyar karɓar haraji ba bisa ƙa'ida ba.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana cewa bayanan sirri sun nuna cewa 'yan ta'addan na amfani da wasu motoci da babura wajen karɓar kuɗaɗe daga fararen hula a yankin.

Sanarwar ta ce bayan samun bayanan sirrin, dakarun sojin sun gudanar da wani sintiri na musamman a yankin Paya Kafiya a ranar 19 ga Yulin 2026.

A yayin arangamar da suka yi da 'yan ta'addan, sojojin sun buɗe musu wuta, lamarin da ya kai ga lalata ɗaya daga cikin motocinsu tare da kashe direban motar.

Rundunar ta kuma bayyana cewa wasu 'yan ta'adda huɗu sun tsere zuwa cikin daji dauke da raunukan harbin bindiga.

A wani samame da dakarun suka ci gaba da kai wa ranar 20 ga Yuli, sun yi nasarar ƙwato makamai, harsasai da kuma wata mota da ake zargin 'yan ta'addan na amfani da ita.

Rundunar sojin ta ce wannan nasara ta taimaka wajen tarwatsa wata muhimmiyar hanyar da Boko Haram/ISWAP ke samun kuɗaɗen gudanar da ayyukansu a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.