Mahukunta a Indonesia sun kama mutane 19 da ake zargi da hannu a safarar jarirai kusan 34 zuwa ƙasashen waje, lamarin da ya sake jawo hankali kan matsalar safarar yara da ke addabar ƙasar.

Binciken hukumomi ya gano cewa wasu daga cikin jariran an sayar da su zuwa ƙasar Singapore kan kuɗaɗe masu yawa.

Wata kotu a Indonesia ta yanke wa shugabar wata ƙungiyar da ake zargi da safarar jariran, Lie Siu Luan mai shekaru 70, hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a gidan yari bayan samunta da laifin safarar mutane.

Masu gabatar da ƙara sun nemi kotun ta yanke mata hukuncin ɗaurin shekaru 10, yayin da ita kuma ta amsa a gaban kotu cewa ta taimaka wajen safarar aƙalla jarirai 12 zuwa Singapore.

Kotun ta kuma yanke wa Astri Fitrinika hukuncin ɗaurin shekaru shida da watanni bakwai saboda hannu a wannan laifi.

Takardun kotu sun nuna cewa a shekarar 2022, Lie ta sayar da wani jariri a Singapore kan kuɗin da ya kai dala dubu 17.

An fara gano wannan lamari ne bayan wasu iyaye sun kai rahoton sace ɗansu ga 'yan sanda a yankin Yammacin Java a shekarar da ta gabata.

Binciken da ya biyo baya ya kai ga ceto wasu jarirai da dama da ake shirin safararsu, yayin da hukumomi suka ce safarar mutane, musamman yara, na ci gaba da kasancewa babbar matsala a Indonesia duk da matakan da ake ɗauka na yaƙi da ita.