Kwamishinan 'Yan Sandan Babban Birnin Tarayya (FCT), Ahmed Sanusi, ya gargadi mazauna Abuja, musamman matasa, da kada su amince jami'an tsaro su binciki wayoyinsu yayin sintiri ko tsayawa domin bincike a kan hanya ba tare da bin ka'idojin doka ba.

Ya ce umarnin Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya ya haramta wa jami'an 'yan sanda binciken wayoyin jama'a ba tare da bin ƙa'ida ba, sakamakon yadda wasu ke amfani da hakan wajen cin zarafi da kuma karɓar rashawa.

Ahmed Sanusi ya bayyana cewa binciken waya na iya gudana ne kawai idan an kama wanda ake zargi da aikata laifi bisa tanadin doka, sannan aka kai shi ofishin 'yan sanda domin ci gaba da bincike.

Ya kuma buƙaci duk wanda wani jami'in tsaro ya nemi ya buɗe wayarsa a hanya ba tare da bin doka ba da ya ƙi amincewa, sannan ya kira layin gaggawa na 'yan sanda ko kuma ya nemi taimakon jami'an da ke kusa.

Kwamishinan ya jaddada cewa Rundunar 'Yan Sandan FCT za ta ci gaba da aiwatar da umarnin Sufeto Janar na 'Yan Sanda tare da hukunta duk wani jami'in da aka kama yana karya wannan doka.