Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci ƙasashen da ke ƙarƙashin Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) su haɗa kai wajen yin Allah wadai da hare-haren ƙyamar baƙi da ake kai wa 'yan Najeriya da sauran 'yan Afirka a ƙasar Afirka ta Kudu.

Tinubu ya ce ya kamata ECOWAS ta gabatar da batun a gaban Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) domin a ɗauki matakin gaggawa kan lamarin.

An bayyana wannan matsaya ne ta bakin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, yayin taron shugabannin ECOWAS karo na 69 da aka gudanar a birnin Freetown na ƙasar Saliyo.

A cewarsa, gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da hare-haren, tana mai cewa shirun diflomasiyya kan irin waɗannan abubuwa na iya ƙarfafa masu aikata su. Ya kuma ce gwamnatin tarayya ta kwashe sama da 'yan Najeriya dubu ɗaya da ɗari huɗu da casa'in daga Afirka ta Kudu ta jiragen sama guda bakwai domin kare rayukansu.

Rahotanni sun nuna cewa Najeriya na ƙoƙarin haɗa kai da Ghana domin matsa wa AU lamba ta ɗauki mataki kan ci gaba da hare-haren ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu.

Baya ga wannan batu, Tinubu ya sake jaddada goyon bayan Najeriya ga shirin ECOWAS Compact for the Future of Regional Integration, wanda ke da nufin ƙarfafa haɗin kan ƙasashen yankin, inganta shugabanci nagari, bunƙasa kasuwanci tsakanin ƙasashe da kuma samar da damammakin ayyukan yi ga matasa.

Shugaban ya ce kare rayukan 'yan Afirka da tabbatar da shugabanci nagari na daga cikin ginshiƙan ci gaban nahiyar.