Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) ta bankado wata jami'ar bogi da ke aiki a cikin wani gida mai dakuna uku a yankin Ilado, da ke ƙaramar hukumar Olorunda LCDA a Jihar Legas.
Hukumar ta ce ta ceto matasa 106 da ake zargin an yaudare su da sunan ba su gurbin karatu, tare da kama wanda ake zargi da kasancewa mamallakin cibiyar bayan gudanar da binciken sirri da ya kai ga kai samame a safiyar Litinin.
Binciken farko ya nuna cewa cibiyar ba ta da rajista, ba ta da sahihin suna ko harabar jami'a, amma tana tallata kanta ta intanet a matsayin cibiyar koyon karatu ta nesa mai alaƙa da wata jami'a a ƙasashen waje.
NSCDC ta bayyana cewa yawancin waɗanda aka ceto, masu shekaru tsakanin 19 zuwa 24, sun fito ne daga jihohi daban-daban na Najeriya da kuma ƙasashen Nijar, Kamaru da Togo. Rahotanni sun nuna cewa sun biya kuɗin shiga da na gudanarwa tsakanin naira dubu 200 zuwa miliyan 1.5, yayin da wasu 'yan ƙasashen waje suka biya tsakanin dala 400 zuwa 500.
Hukumar ta kuma ce bincike ya nuna cewa ana tilasta wa waɗanda ke cikin shirin su riƙa kawo sababbin ɗalibai domin samun kuɗi, lamarin da ta ce yana da alamun tsarin damfara irin na Ponzi.
Kwamandan NSCDC na yankin Badagry, CSP Gbenga Ekunola, ya ce za a ci gaba da bincike domin gano sauran masu hannu a lamarin da kuma tabbatar da ko akwai irin wannan zamba a wasu sassan ƙasar. Ya ƙara da cewa za a gurfanar da duk wanda aka samu da laifi a gaban kotu, yayin da za a haɗa waɗanda aka ceto da iyalansu bayan kammala bincike.