Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya nuna rashin jin daɗinsa kan rashin halartar aiki da wuri da wasu manyan jami'an gwamnati suka yi bayan wata ziyarar bazata da ya kai Sakatariyar Gwamnatin Jihar da ke Dutse.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Garba Muhammad, ya fitar, an ce gwamnan ya tarar da ofisoshin wasu manyan jami'ai a kulle, yayin da da dama daga cikinsu ba su halarci aiki ba har zuwa misalin ƙarfe 11 na safe.

Sanarwar ta ce ziyarar na daga cikin rangadin sa ido da gwamnan ke yi domin duba yadda ma'aikata ke kiyaye lokaci, halartar aiki da kuma inganta gudanar da ayyukan gwamnati.

Ta ƙara da cewa matakin ya nuna aniyar gwamnatin Umar Namadi na tabbatar da ladabtarwa, riƙon amana da inganta aikin gwamnati a faɗin jihar.

Bayan ziyarar sakatariyar gwamnatin, gwamnan ya wuce ƙaramar hukumar Ringim domin jajanta wa iyalan waɗanda hatsarin kwale-kwale ya rutsa da su a ƙauyen Malamawar 'Yan Dutse, inda ya halarci jana'izar waɗanda aka gano gawarwakinsu tare da yin addu'a ga mamatan.

Daga bisani, Gwamna Namadi ya duba ayyukan tituna da sauran manyan ayyukan raya ƙasa da ake gudanarwa a Sankara, Kanya Babba da Kazaure, ciki har da asibitoci, cibiyar bincike ta jihar da kuma Kwalejin Fasahar Sadarwa da Bayanai ta Jigawa.