Cutar Ebola da ke ɓulla a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta bazu zuwa yankunan kiwon lafiya 47 da ke faɗin larduna biyar na Adja a lardin Ituri, a cewar hukumomin lafiya.

Alƙaluman da aka fitar a ranar 19 ga Yuli sun nuna cewa an tabbatar da mutum 2,423 sun kamu da cutar, yayin da mutum 967 suka rasu, lamarin da ya sa adadin mace-macen ya kai kusan kashi 39.9 cikin 100.

A cikin sa'o'i 24 da suka gabata, an samu sabbin mutum 79 da suka kamu da cutar, tare da mutuwar mutum 37, inda mafi yawansu suka fito daga lardin Ituri.

Rahotannin sun nuna cewa yankunan Bunia, Nizi, Rwampara da Adja ne suka fi samun sabbin masu kamuwa da cutar.

Hukumomin lafiya sun ce ana ci gaba da bibiyar kashi 81.1 cikin 100 na mutanen da suka yi mu'amala da masu cutar, sai dai sun bayyana cewa har yanzu akwai giɓi wajen gudanar da wannan aiki musamman a lardin Haut-Uélé.

An ayyana ɓullar cutar ne a ranar 15 ga Mayu, kuma ƙwayar cutar da ake kira Bundibugyo ebolavirus ce ke haddasa annobar.

Hukumomin sun ƙara da cewa matsalolin tsaro, yawan zirga-zirgar jama'a da kasuwancin kan iyaka da Uganda da Sudan ta Kudu na ci gaba da kawo cikas ga ƙoƙarin shawo kan yaɗuwar cutar.

Sun kuma yi kira da a ƙara ɗaukar matakan sa ido da kariya domin dakile annobar.