Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar a zaɓen 2027, Peter Obi, ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da ta tanadi cewa zai yi wa'adi ɗaya kacal idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a shirin Politics Today na tashar Channels Television a ranar Litinin.
A cewarsa, yarjejeniyar na daga cikin tubalan haɗakar siyasar da jam'iyyar ta gina domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
Ya kuma bayyana cewa yana da cikakken yaƙinin Peter Obi zai cika alkawarin da ya ɗauka, yana mai bayyana shi a matsayin ɗan siyasa mai gaskiya kuma mai kishin Najeriya.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Peter Obi ko jam'iyyar NDC ba su fitar da wata sanarwa da ke ƙarin bayani ko tabbatar da wannan yarjejeniya ba.