Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) ta sanar da fara bincike kan rikicin da ya biyo bayan wasan ƙarshe na gasar cin Kofin Duniya.

Hukumar ta ce ta miƙa batun ga kwamitinta na ladabtarwa domin gudanar da cikakken bincike kan abin da ya faru a filin wasa na MetLife bayan kammala wasan.

FIFA ta bayyana cewa idan binciken ya tabbatar da laifin wani ɗan wasa ko jami'in tawaga, za a ɗauki matakin ladabtarwa da ya dace bisa tanadin dokokinta. Haka kuma, ana iya ɗaukar mataki kan Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Argentina idan an tabbatar da cewa tawagarta ta karya ƙa'idojin gasar.

Rahotanni sun ce bayan Spain ta doke Argentina da ci 1-0 a wasan ƙarshe da aka buga ranar Lahadi, wasu 'yan wasan Argentina da jami'an tawagar suka shiga rikici da 'yan wasan Spain yayin da suke murnar nasarar da suka samu.

Daga cikin waɗanda aka ce an gani a wurin rikicin akwai Nahuel Molina, Leandro Paredes, Thiago Almada da mataimakin kocin Argentina, Roberto Ayala.

Ana sa ran FIFA za ta bayyana sakamakon binciken da kuma duk wani matakin ladabtarwa bayan kammala binciken.