'Yar kasuwa kuma shugabar kamfanin Oceangate Engineering Oil & Gas Limited, Aisha Achimugu, ta zargi Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da muzgunawa, bata mata suna da kuma kwace wasu kadarorinta ba bisa ƙa'ida ba.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, Achimugu ta ce bayanan da EFCC ke yaɗawa sun jawo mata asarar damammakin kasuwanci tare da jefa rayuwarta, ta iyalanta da kuma jarin da ta zuba cikin haɗari.
Ta kuma yi zargin cewa jami'an EFCC sun kai samame gidanta sau biyu, inda suka kwashe kayan ado, kuɗaɗe da motoci, tare da cewa an ci zarafin iyalanta yayin gudanar da samamen.
Achimugu ta ce dala miliyan 13 da kotu ta bayar da umarnin a ƙwace na daga cikin dala miliyan 20 da kamfaninta ya biya Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta Najeriya (NUPRC) domin biyan kuɗin lasisin rijiyoyin mai. Ta ce ta ɗaukaka ƙara kan wannan hukunci.
Har ila yau, ta yi zargin cewa matakan da EFCC ta ɗauka sun haddasa soke mata takardar izinin shiga Amurka, lamarin da ya hana ta halartar wani shirin horaswa a Jami'ar Harvard.
Sai dai EFCC na ci gaba da tuhumar Aisha Achimugu da laifukan da suka haɗa da safarar kuɗaɗe. Haka kuma, kotuna sun bayar da umarnin ƙwace wasu kuɗaɗe da kadarorin da ake dangantawa da ita ga Gwamnatin Tarayya, yayin da ake ci gaba da sauraron shari'ar.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, shari'ar na ci gaba da gudana a kotu, kuma ba a yanke hukunci na ƙarshe kan zarge-zargen ba.